9 Nuwamba 2015 - 13:51
Buhari zai rantsar da Ministocinsa a ranar Laraba

A jibi Laraba ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai rantsar da sabbin ministoci na farko a gwamantinsa, abin da zai kawo karshen zaman jira na watanni biyar da al’ummar kasar ke yi tun bayan rantsar da shugaban akan mukaminsa.

A cikin wata Sanarwa, mai Magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina, ya bayyana cewa da misalin karfe 10 na safiyar Laraba ne shugaba Buhari zai kaddamar da sabuwar majalisar ministocinsa, kuma kafin nan kowane daga cikin ministocin 36 zai karbi rantsuwar kama aiki.

Tuni dai Shugaba Buhari ya gana da Ministocin inda ya jaddada masu alkiblar gwamnatinsa na tabbatar da canji a Najeriya.

‘Yan Najeriya dai sun zura ido yanzu su ji ma’aikatun da za a ba Ministocin, musamman wadanda ke da muhimmaci ga tafiyar canji ta gwamnatin Buhari. 289